Yawan Al'ummar Najeriya Ya Haura Miliyan 193
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i15901-yawan_al'ummar_najeriya_ya_haura_miliyan_193
Hukumar kula kididdigar al'umma ta kasa a Najeriya ta fitar da wani rahoto a yau Juma'a inda ta bayyana cewa yawan al'umma a kasar ya tasamma Miliyan 193,3.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Dec 30, 2016 12:03 UTC
  • Yawan Al'ummar Najeriya Ya Haura Miliyan 193

Hukumar kula kididdigar al'umma ta kasa a Najeriya ta fitar da wani rahoto a yau Juma'a inda ta bayyana cewa yawan al'umma a kasar ya tasamma Miliyan 193,3.

Tun fil azal ma Najeriya ita ce ta kasance kasa mafi yawan al'umma a Nahiyar Afrika.

Hukumar NBS dai ta fitar da wadanan alkaluma ne bisa kididigar da kwamitin kasar mai kula da al'umma ya yi a cikin shekara 2006 a lokacin da kasar keda yawan al'umma Miliyan 140.4.

Rahoton dai ya ambato jihar Kano dake arewacin kasar wace ta fi yawan al'umma inda take da mutane Miliyan 13, yayin da jihar Lagos keda Miliyan 12,5 duk da cewa gwamnatin Lagos na tantama akan wadanan al'kalumen inda take cewa yawan al'ummar dake rayuwa a cikin jihar wace akeyi wa kallon cibiyar kasuwancin yammacin Afrika, ya kai Miliyan 22.

Marabin dai da ayi takaimaiman kididigar al'umma a Najeriya tun shekaru goma da suka gabata.

Rahoton karshe dai na hukumar ta NBS ya nuna cewa mafi akasarin al'ummar Najeriya yara ne, kuma daga cikinsu Miliyan 58 'yan kasa da shekara tara ne.