Shugaban Kasar Turkiya Ya Ziyarci Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i1594-shugaban_kasar_turkiya_ya_ziyarci_najeriya
Shugaba Rajab Tayyib Urdogan Na Turkiya Ya Ziyarci Kasashen Najeriya Da Ghana
(last modified 2018-08-22T11:27:53+00:00 )
Mar 03, 2016 07:39 UTC
  • Shugaban Kasar Turkiya Ya Ziyarci Najeriya

Shugaba Rajab Tayyib Urdogan Na Turkiya Ya Ziyarci Kasashen Najeriya Da Ghana

A jiya laraba ne dai shugaban na kasar Turkiya ya ziyarci Najeriya inda ya gana da takwaransa Muhammadu Buhari a birnin Abuja.

Shugaban kasar ta Turkiya wanda ya gabatar da taron manema labaru na hadin guiwa da shugaba ya ce; Ta'addanci ba shi da addini, kuma babu wani banbanci a tsakanin dukkanin 'yan ta'adda."

Dangane da alakar kasarsa da Turkiya kuwa, shugaban kasar ta Turkiya ya ce; Najeriya kasa ce mai babbar kasuwa, saboda haka alaka da kasar Turkiya tana da muhimmanci.

Har ila yau, shugaba Urdogan ya bayyana cewa; Kamfanonin kwangila na Turkiya a shirye su ke su yi a Najeriya, musamman saboda la'akari da cewa sun sami nasarar zama na biyu a duniya.