An Kashe Wani Babban Jami'in Tsaro A Fadar Shugaban Kasar Somalia
Wasu majiyoyin gwamnatin kasar Somalia ta bayyana cewa wani harbi da bindiga a fadar shugaban Somalia ya yi sanadiyya mutuwar mataimakin shugaban sojojin da suke kare fadar shugaban kasa.
Kamfanin dillancin labaran World Bulletin ya nakalto daga wata majiyar a fadar shugaban kasar ta Somalia a birnin Magadishu tana cewa wani soja a fadar ya bindige Abdi Abdilla mataimakin shugaban sojoji masu kare fadar shugaban har lahira.
Labarin ya kara da cewa wanda ya aikata wannan mummunan aiki ya yi kokarin arcewa daga fadar amma sauran sojoji masu gadin fadar suka capke shi da ransa.
Majiyar fadar shugaban kasar ta tabbatar da cewa babu wanda wanda abin ya shafa in banda shi Abdi abdillah. Kuma kome ya koma kamar yadda yake a fadar. Majiyar bata bayyana ko su waye suka kai harin ba, sannan babu wanda ya dauki nauyi kai harin ya zuwa yanzu
A shekara ta 2014 dai mayakan kungiyar yan ta'adda ta Al-shaba sun taba kai hari a kan fadar ta shugaban kasa.