Shugaban Kasar Gambia Ya Zargi ECOWAS Da Shelanta Yaki A Kan Kasarsa
(last modified Sun, 01 Jan 2017 15:51:41 GMT )
Jan 01, 2017 15:51 UTC
  • Shugaban Kasar Gambia Ya Zargi ECOWAS Da Shelanta Yaki A Kan Kasarsa

Shugabann kasar Gambia Yahayah Jemeh ya bayyana cewa kungiyar raya tattalin arziki na yammacin Afrika ECOWAS ta shelanta yaki a kan kasarsa.

Kamfanin dillancin Labaran reuters ya nakalto shugaba Yahyah  Jameh yana fadar haka ne a jawabinsa na sabuwar shekara ta 2017 a jiya da dare. Shugaban ya kara da cewa kasar Gambia ba ta son yaki amma in ya zama dole ta kare kanta daga mamayar bakin aure bata da zabi.

Banda haka dai shugaban ya kara da cewa matsayin da kungiyar ECOWAS ta dauka na cewa a shirye take ta kauda shi da karfin tuwa daga shugabancin kasar idan ya ki sauka a karshen wannan watan, wani mataki ne na raina kundin tsarin mulkin kasar ta Gabia.

Shugaba Jameh dai ya amince da faduwa a zaben ranar daya ga watan Decemban shekarar da ta gabata sanna daga baya ya dawo ya ce an yi magudi don haka bai amince da sakamakin zaben ba.

Kungiyar ECOWAS dai tun farko ta aike da tawaga karkashin shugaban kungiyar da kuma wasu  shuwagabannin kasashen yankin zuwa birnin Banjul don tattaunawa da shugaban amma sun kasa shawo kansa.