An yi Kira Da A Saki Sheikh Zakazaky A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i15997-an_yi_kira_da_a_saki_sheikh_zakazaky_a_najeriya
Kungiyar Harkar Musulmi A Najeriya Ta yi Kira Da A Saki Shugabanta Sheikh Ibrahim Yakub El-zakzaky.
(last modified 2018-08-22T06:59:28+00:00 )
Jan 02, 2017 08:17 UTC
  • An yi Kira Da A Saki Sheikh Zakazaky A Najeriya

Kungiyar Harkar Musulmi A Najeriya Ta yi Kira Da A Saki Shugabanta Sheikh Ibrahim Yakub El-zakzaky.

Kungiyar 'Yan'uwa Musulmi a Najeriya Ta yi Kira da A saki Shugabanta Sheikh Ibrahim Yakub El-zakzaky.

Kakakin kungiyar ta harkar musulmi a Najeriya, Ibrahim Musa,  da ya ke maida martani akan jawabin shugaban kasar Muhammadu Buhari dangane da sakon sabuwar shekara, ya bukaci shugaban kasar da ya yi aiki da umarnin Kotu na sakin Sheikh Ibrahim El-zakzaky.

Bugu da kari, Ibrahim Musa ya bukaci ganin shugaban kasar ta Najeriya ya sa an binciki kisan da aka yi wa mambobin harkar ta musulunci.

Daruruwan mutane ne dai sojojin kasar su ka kashe a harin da su ka kai a Husaniyar Bakiyyatullah a 2015 da kuma gidan Sheikh Ibrahim Yakubu El-zakzaky.