Mozambique : Renamo Ta Shelanta Tsagaita Wuta Da Wata Biyu
Babbar jam'iyyar adawa a kasar Mozambique (Renamo) ta sanar da dakatar da bude wuta har na tsawon wata biyu a wani mataki na share fagen shirin tattaunawa zamen lafiya da gwamnatin kasar.
Dama kafin hakan, kungiyar ta na cikin wani shirin tsagaita wuta na mako biyu wanda ta ce tayi sa ne domin baiwa al'ummar kasar ta Mozambique damar gudanar da bukukuwan karshen shekara cikin kwaciyar hankali.
A wannan Talata shugaban kungiyar Afonso Dhlakama ya ce za'a tsawaita shirin har tsawan kwanaki 60, wato har zuwa 4 ga watan Maris na wannan shekara.
kawo yanzu gwamatin kasar bata ce uffan ba kan wannan matakin ba zata na Renamo, aman a ranar Litinin data gabta shugaban kasar Filipe Nyusi, ya ce batun tsawaita shirin tsagaita wuta yauni ne daya rataya ga kungiyar 'yan adawan masu dauke da makamai ta Renamo.
Sannan ya kara da cewa hanyar da kungiyar ta Renamo ta dauko mai kyawo ce kuma zata taimaka wajen samun fahimtar juna tsakanin ta da gwamnati kamar dai yadda ya fada a gidan talabijin din kasar na STV .