Sudan : An Kara Wa'adin Tsagaita Wuta
Shugaban kasar Sudan Omar Hassan Al Bashir, ya sanar da tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta na tsawon wata guda a fadan da dakarunsa ke yi da ‘yan tawaye a yankin Darfur.
Tun a watan Oktoban 2016 ne, bangarorin biyu suka amince da tsagaita bude wuta a yankunan kudancin Blue Nile da Kordufan, amma har yanzu ana samun rikici a Dafur.
Rahotanni sun ce wasu ‘yan bindiga sun bude wuta a Nertiti, yankin Darfur, in da suka kashe mutane 8 yawancinsu mata da aka bindige a cikin gida.
Tun a 2011 ne sabon fada ya barke tsakanin dakarun Sudan da ‘yan tawaye a Kordufan da Blue Nile, a lokacin da Sudan ta kudu ta balle daga kasar.
An dai dade ana kokarin sulhu domin samun zaman lafiya kuma wannan ne ya sa shugaban ya kara tsawaita tsagaita wuta a sakon sabuwar shekara domin bude kofar sasantawa da ‘yan tawayen a Darfur.