Gwamnatin Kenya Za Ta Bunkasa Ayyukan Bankin Muslunci A Kasarta
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i16108-gwamnatin_kenya_za_ta_bunkasa_ayyukan_bankin_muslunci_a_kasarta
Gwamnatin kasar Kenya ta sanar da cewa, tana shirin bunkasa ayyukan bankin musluci a kasar, da sauran ayyukan tattalin arziki da suke da alaka da wannan baki domin kara bunkasa tattalin arzikin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:29+00:00 )
Jan 04, 2017 14:23 UTC
  • Gwamnatin Kenya Za Ta Bunkasa Ayyukan Bankin Muslunci A Kasarta

Gwamnatin kasar Kenya ta sanar da cewa, tana shirin bunkasa ayyukan bankin musluci a kasar, da sauran ayyukan tattalin arziki da suke da alaka da wannan baki domin kara bunkasa tattalin arzikin kasar.

Jaridar Daily Nation ta kasar Kenya ta bayar da rahoton cewa, shugaban kasar ta Kenya Uhuro Kenyatta ya bayyana cewa, yana da zimmar aiwatar da wani sabon shiri na bunkasa harkokin tattalin arzikin kasar ta hanyar gudanar da ayyukan hadin gwiwa tare da bankin muslunci.

Kenyatta ya ce ko shakka babu za a amfana matuka a kasar Kenya da tsarin ayyukan bankin musulunci, domin kuwa akwai abubuwa da dama wadanda suka shafi harkokin zuba hannayen jari da ayyuka wadanda za su amfani kasar Kenya ta hanyar wannan baki.

Ya kara da cewa, yanzu haka magana ta yi nisa a tsakaninsu da manyan cibiyoyi a kasar Malaysia da suke da manyan hannayen jari a bankin muslucni, dangane da yadda za su yi aiki tare da kasar Kenya, wanda kuma a cewarsa, hakan zai bude kofa ga sauran kasashen Afirka su ci moriyar ayyukan bankin muslunci, domin kuwa a cewar Uhuru Kenyatta akwai abubuwa da dama da aka yi musu mummunar fahimta dangane da wanann banki, amma masana harkokin tattalin arziki sun yi imanin cewa suna da amfani, akan haka Kenya za ta zama a sahun gaba wajen yin mu'amala da wannan banki.