Marocco : An Ceto Bakin Haure 45 A Gabar Ruwan Nador
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i16126-marocco_an_ceto_bakin_haure_45_a_gabar_ruwan_nador
Hukumomin a kasar Marocco sun sanar da ceto wasu bakin haure 45 'yan asalin yankin Kudu da hamadar sahara a gabar ruwan Nador dake arewa maso gabashin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:29+00:00 )
Jan 05, 2017 08:26 UTC
  • Marocco : An Ceto Bakin Haure 45 A Gabar Ruwan Nador

Hukumomin a kasar Marocco sun sanar da ceto wasu bakin haure 45 'yan asalin yankin Kudu da hamadar sahara a gabar ruwan Nador dake arewa maso gabashin kasar.

Sanarwar ta kuma ce an tsamo gawawakin mutane uku ciki har da gawar wata 'yar karamar yarinya.

Birnin Nador dai na kusa ne da wasu yankunan na Melina mallakar kasar Espaniya da ya raba iyaka da kasashen Turai da na Afrika.

Tun dai a tsakiyar watan Disamba ne hukumomin Marocco suka kaddamar da wani shiri na farautar bakin haure dake neman shiga turai ba bisa ka'ida ba.