Ivory Coast : Sojoji Sunyi Bore A Bouake
Jan 06, 2017 07:01 UTC
Tsaffin 'yan tawayen da aka shiggar aikin soji a Ivory Coast na bore a Bouake, birnin na biyu mafi girma a kasar.
Rahotanni daga kasar sun ce sojojin sun farmawa wasu offishin 'yan sanda biyu a birnin inda suka kwashi bindigogi da motoci suka bazu cikin tutuna tare da toshe hanyoyi.
Wani soji daya bukaci kanfanin dilancin labaren AFP ya sakaya sunansa ya shaida cewa sojojin na bore ne domin neman wasu kudaden alawus Miliyan biyar na CFA kwatamcin kudin Euro (7,600) da kuma gida ko wannensu.
Tun da farko dai an jiyo karan harbin mayan makamai da sanyin safiyar nan a kusa da babbar barikin sojin Bouake na kasar ta Ivory Coast.
Tags