Za'a Koma Zaman Shari'a Hissen Habre Ran Litinin
A Ranar Litinin mai zuwa ce za'a yi zaman shari'a tsohon shugaban mulkin kama karyar na kasar Chadi Hissene Habre bayan da ya daukaka kara kan hukuncin rai da rai da aka yanke masa a watan Mayu shekara data gabata.
Saidai bayanai sun nuna cewa da wuya za'a gabatar da Mista Habre a zamen na ranar Litinin idan dai ba wasu shaidu aka samu ba.
Kotun musamman ta hukunta manyan lafukan yaki ta Afrika mai cibiyarta a birnin Dakar na kasar Senegal ta yanke hukuncin zaman kason rai da rai ga tsohon shugaban mulkin kama karyar kasar Chadi Hissene Habre, bayan da ta same shi da aikata laifuka da dama da suka hada da na hallaka jama'a dama fyade a kasarsa lokacin da ya ke mulki.
Bayan hukuncin Mr Habre ya daukaka kara yana mai cewa ba'a masa adalci ba.