Gwamnatin Sudan Ta Kudu Ta Tabbatar Da Kashe Kwamandan 'Yan Tawayen Kasar
Gwamnatin kasar Sudan ta kudu ta tabbatar da kashe kwamandan daya daga cikin manyan kungiyoyin 'yan tawayen kasar Janar Gabriel Tanginye bayan wani musayen wuta da ya gudana tsakanin kungiyoyi masu dauke da makami a yankin Upper Nile na kasar.
Kafar watsa labaran Africanews ta bayyana cewar ministan watsa labaran kasar Sudan ta Kudun, Michael Makuei ne ya sanar da hakan a wata ganawa da yayi da manema labarai a birnin Juba, babban birnin kasar Sudan ta Kudu, inda ya ce dakarun Janar Johnson Olony ne suka kashe Janar Tanginyen a wani musayen wuta da ya gudana a tsakaninsu.
Rahotanni dai sun ce kimanin mutane ashiri ne aka kashe yayin wannan rikici da ya barke tsakanin kungiyoyin 'yan tawayen biyu. Sai dai har ya zuwa yanzu ba a tantance mene ne musabbin rikicin da ya barke a tsakaninsu ba, sai dai ana ganin da ya wuya in ba kokari ne na neman iko ta tabbatar da mulki ba.
Shi dai Janar Gabriel Tanginye yana daga cikin manyan kwamandojin babban kungiyar 'yan tawayen Sudan ta Kudun ta Sudan People’s Liberation Army karkashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudun Riek Machar jim kadan bayan sanya hannun da yayi kan yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin kasar.