Ivory Coast : An Kori Mayan Jami'an Tsaro
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i16351-ivory_coast_an_kori_mayan_jami'an_tsaro
Shugaban kasar Ivory Coast / Cote d'Ivoire, Alhassane Ouattara, ya sallami manyan jami'an tsaro kasarsa da suka hada dana Soji, 'yan sanda da kuma Jandarma daga bakin aiki.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Jan 10, 2017 03:05 UTC
  • Ivory Coast : An Kori Mayan Jami'an Tsaro

Shugaban kasar Ivory Coast / Cote d'Ivoire, Alhassane Ouattara, ya sallami manyan jami'an tsaro kasarsa da suka hada dana Soji, 'yan sanda da kuma Jandarma daga bakin aiki.

Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar wace aka karanto a gidan talabijin din kasar a Jiya Litinin ta ce shugaba Ouatara ya dakatar da aikin babban hafsan sojin kasar Janar Soumaïla Bakayoko, da babban hafsan jami'an tsaro Jandarma Gervais Kouakou kouassi, da kuma babban darectan 'yan sanda na kasar Bredou M’Bia.

Amman shugaba Watara ya jinjinawa mayan jami'an tsaron a cikin sanarwar.

Saidai sanarwar ba tayi karin bayyani ba akan dalilin daukan wannan matakin na shugaba Ouatara, amma matakin na zuwa kwana guda bayan bore da sojojin suka yi a wasu manyan birane na kasar ciki har da Bouake da Abidjan babban birnin kasar.

Sanarwar ta kuma zayyano sunayen sabbin jami'an da zasu maye gurbbin wadanda aka sallama.

Wannan dai na zuwa ne bayan da shugaban kasar ya amince da murabus din firaministansa Daniel Kablan Duncan, da gwamnatinsa wata guda bayan da kawacen jam'iyyu masu mulki suka samu rinjaye a zaben 'yan majalisar dokokin kasar.