Kananan Yara Kimanin 60,000 Suna Fuskantar Barazanar Mutuwa A Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i1639-kananan_yara_kimanin_60_000_suna_fuskantar_barazanar_mutuwa_a_somaliya
Jami'in Majalisar Dinkin Duniya mai kula da harkokin jin kai a yankin arewa maso gabashin nahiyar Afrika ya bayyana cewa: Kananan yara kimanin 60,000 ne suke fuskantar barazanar mutuwa a kasar Somaliya saboda rashin kayayyakin jin kan bil-Adama.
(last modified 2018-08-22T06:57:54+00:00 )
Mar 03, 2016 16:15 UTC
  • Kananan Yara Kimanin 60,000 Suna Fuskantar Barazanar Mutuwa A Somaliya

Jami'in Majalisar Dinkin Duniya mai kula da harkokin jin kai a yankin arewa maso gabashin nahiyar Afrika ya bayyana cewa: Kananan yara kimanin 60,000 ne suke fuskantar barazanar mutuwa a kasar Somaliya saboda rashin kayayyakin jin kan bil-Adama.

Jami'in Majalisar Dinkin Duniya mai kula da harkokin jin kai a yankin arewa maso gabashin nahiyar Afrika Peter de Clark matsalolin tashe-tashen hankula da fari da kuma ambaliyar ruwa da ake samu a yankuna daban daban na kasar Somaliya, hakan ya wurga mutane cikin halin kaka-ni ka yi, inda akwai mutane da yawansu ya doshi miliyan biyar da suke bukatar kayayyakin jin kai.

De Clark ya kara da cewa; Daga cikin mutanen da suke tsananin bukatar tallafin gaggawa a Somaliya akwai kananan yara kimanin 60,000 wanda sakacin aikewa da taimakon gaggawa cikin hanzari zai kai ga hasarar rayukansu.