Kenya : An Daure Wakilan Kungiya Saboda Yajin Aikin Likitoci
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i16513-kenya_an_daure_wakilan_kungiya_saboda_yajin_aikin_likitoci
Wata kotu a kasar Kenya ta yanke hukuncin daurin talala na wata guda ga wasu wakilan kungiya tare da basu umurnin dakatar da yajin aikin da likitoci suka shafe kusan kwanaki 40 suna yi a kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:31+00:00 )
Jan 12, 2017 12:21 UTC
  • Kenya : An Daure Wakilan Kungiya Saboda Yajin Aikin Likitoci

Wata kotu a kasar Kenya ta yanke hukuncin daurin talala na wata guda ga wasu wakilan kungiya tare da basu umurnin dakatar da yajin aikin da likitoci suka shafe kusan kwanaki 40 suna yi a kasar.

Mai shari'a, Hellen Wasilwa, ta baiwa likitocin da wakilansu mako guda na su koma bakin aiki idan ba haka ba za'a dakatar da wakilan bakwai a kuma dauresu a gidan yari.

Saidai a cewar shugaban kungiyar likitocin ta (KPMDU) Ouma Oluga, wannan matakin bai zai katse masu hamzari ba, kuma zasu ci gaba da yajin aikin idan gwamnati bata biya masu bukatu ba.

A zamen data yi yau Alhamis kotun ta Kenya ta baiwa gwamnatin kasar dake cewa yajin aikin da likitocin keyi baya bisa ka'ida gaskia, saboda ana cikin tattaunawa.

Saidai likitocin su kimanin 5,000 na asibitocin gwamnati da suka tsunduma yajin aiki tun ranar biyar ga watan Disamban shekara data gabata sun ce har yanzu gwamnati bata waiwaye su ba akan bukatocin da suka gabatar a yarjejeniyar da suka cimma da gwamnatin tun cikin shekara 2013.

Likitocin dai na bukatar a linka masu albashinsu da suke dauka har sau hudu, inda ko a ranar Juma'a data gabata sukayi watsi da wani tayin gwamnati na karin kashi arba'in cikin dari akan albashinsu.