Amurka Zata Sassautawa Sudan Takunkuman Tattalin Arziki
(last modified Fri, 13 Jan 2017 16:04:56 GMT )
Jan 13, 2017 16:04 UTC
  • Amurka Zata Sassautawa Sudan Takunkuman Tattalin Arziki

A dai dai lokacinda gwamnatin shugaban Umar Hassan Al-bashir na kasar Sudan take kokarin kyautata dangantakarta da kasar Amurka , gwamnatin Amurka ta bada sanarwan cewa zata sassautawa kasar takunkuman da ta dora mata

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto wani jami'in diblomasiyar kasar Amurka yana fadar haka a yau jumma'a ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar zata sassautawa kasar Sudan takunkuman da ta dora mata, daga ciki akwai na zuba jari da kasuwanci. 

Jami'in ya kara da cewa gwamnatin Amurka ta dau wannan matakinne don irin ci gaban da aka samu a cikin matsalolin da suka jawo dorawa sudan takunkuman. 

Labarin ya kara da cewa amma matsalar laifuffukan yakin da ake zargin shugaban kasar ta Sudan Umar Hassan al-bashir da kuma kasancewar kasar sudan cikin jerin kasashe masu tallafawa ayyukan ta'addanci zasu ci gaba kamar yadda suke.

A cikin watan Nuwamban da ya gabata ne gwamnatin kasar ta Amurka ta sabonta takunkuman da ta dorawa kasar ta Sudan na wata shekara guda.