Ivory Coast : An Cimma Yarjejeniyar Karshe Da Sojoji Masu Bore
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i16561-ivory_coast_an_cimma_yarjejeniyar_karshe_da_sojoji_masu_bore
Rahotanni daga kasar Ivory Coast na cewa gwamnatin kasar ta cimma yarjejeniyar karshe da sojoji da ke bore akan batun biyan albashi da kuma alwasus, bayan da ake sake shiga halin rashin tabas a Birnin Bouake inda sojojin suka kwashe wunin jiya suna harbe-harbe.
(last modified 2018-08-22T06:59:32+00:00 )
Jan 14, 2017 02:52 UTC
  • Ivory Coast : An Cimma Yarjejeniyar Karshe Da Sojoji Masu Bore

Rahotanni daga kasar Ivory Coast na cewa gwamnatin kasar ta cimma yarjejeniyar karshe da sojoji da ke bore akan batun biyan albashi da kuma alwasus, bayan da ake sake shiga halin rashin tabas a Birnin Bouake inda sojojin suka kwashe wunin jiya suna harbe-harbe.

An cimma wannann yarjejeniyar ce a Bouake tsakanin babban hafsan sojin kasar da ministan tsaro da kuma wakilan sojojin masu bore kamar yadda wata majiyar gwamnati ta shaidawa kanfanin dillancin labaren AFP.

A yayin da ake tattaunawa domin cimma yarjejeniyar, an ji karar harbe-harben bindiga a wasu birane da ke sassan kasar ,yayinda sojojin da ke boren kuma suka kewaye Bouake inda ake tattaunawar.

An dai rawaito sojojin na nuna farin cikinsu dangane da cimma wannan yarjejeniya, koda yake basu so yin karin haske ba akan abunda yarjejeniyar ta kunsa.

Bayanai daga kasar sun ce sojojin sun koma barikinsu kuma an daina jin karen harbe-harbe bayan cimma wannan yarjejeniyar wace ita ce ta biyu da aka cimma tsakanin bangarorin a cikin mako guda.

A makon daya gabata ne sojojin wadanda tsayin 'yan tawaye ne da aka shigar dasu aikin soji suka fara bore a birnin Bouake wanda shi ne birni na biyu mafi girma a kasar, kafin daga bisani boren ya bazu zuwa wasu sassan kasar ciki har da Abidjan babban birnin kasar.