Matsalar Kiwan Lafiya Na Bijirowa Wadanda Suka yi Jinyar Ebola
Wani bincike na masana sha'anin kiwan lafiya ya nuna cewa uku daga cikin hudu na mutanen da suka yi jinyar cutar Ebola na fama da matsalar kiwan lafiya.
Binciken da cibiyar (The Lancet Infectious Diseases) ta rawaito ya nuna cewa kashi 18 cikin 100 na wadanda suka yi jinyar cutar Ebola na fama da matsalar gani wanda ke kaiwa har zuwa dundumi.
Wannan kuma ya ci karo da rahoton wani gagarimin bincike da ake yi a kasar Guinea wanda shi ma ya nuna irin wadannan alamun.
A kasar Saliyo an samu mutane 277 da suma suka nuna wasu alamomi watanni hudu bayan da suka warke daga cutar.
Wani sashe na binciken ya nuna cewa shekara guda bayan jinya cutar kashi 40% na mutanen na fama da gajiya ko zazzabi, sanan kashi 38% na fama da matsalar ciwan gababuwan jiki, yayin da kashi 35% ke fama da ciwan kai, yayin da kashi 2% suka samu matsalar ji, sai kuma kashi 26% wandanda ke fama da karamcin jini.
Wannan dai shi ne karo na farko da aka gudanar da binciken gama gari kuma cikin dogon lokaci ga wadanda suka yi jinyar cutar Ebola ciki har da yara a cewar Dr Eric Delaporte na kasar faransa daya jagoranci binciken.
Masanan sun ce koda yake matsalar ta biyo bayan shekara guda na jinya abun damuwa ce.
An kiyasta mutane 17,000 da suka yi jinyar cutar Ebola a lokacin annobar ta bazu a yankin yammacin Afrika.