An Sace Yan Makaran Da Malamansu A Wata Makaranta A Nigeria
Majiyar yansandan Nigeria daga Jihar Ogun daga kudancin kasar ta bayyana cewa wasu yan bindiga sun sace yan makaranta 5 da malamansu biyu a wata makaran a jihar.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa yan bindigan sun sace yan makarantan 6 da malamansu guda biyu, daya daga cikinsu dan kasar turkia ne a safiyar Jumma'a, kuma har yanzun babu labarinsu.
Kakakin yansanda na jihar Abimbola Oyeyemi ya fadawa Reuters cewa tuni yansanda a jihar sun tura ma'aikatansu don gani wadanda aka sacen da kuma dawo dasu gida lafiya ba tare da ko kwarzani ba, sannan akwai batun hukunta wadanda suka aikata wannan laifin.
Makarantar wacce ta kasa da kasa she tana da malaman daga kasashen waje, wadanda suke karantarwa da kuma gudanar da ayyukan hurar da dalibai.
Labarin ya kara da cewa a cikin watan satumban da ya gabata ma wasu yan bindigan sun sace mutanen kasar China biyu amma jami'an yan sanda sun kubutar da su.