Kasar Masar Ta Dakatar Da Zirga Zigan Jiragen Saman Kasar Zuwa Saudia
(last modified Sun, 15 Jan 2017 11:48:45 GMT )
Jan 15, 2017 11:48 UTC
  • Kasar Masar Ta Dakatar Da Zirga Zigan Jiragen Saman Kasar Zuwa Saudia

Gwamnatin kasar masar ta bada sanarwan dakatar da zirga zirgan jiragen saman kasar zuwa kasar saudia a saufiyar yau lahadi.

Shafin yanar gizo na labarai mai suna (وابه الفجر) ya nakalto majiyar tashar jiragen sama na 5 a birnin Alkahira kan cewa ta dakatar da tashin jiragen saman kasar ta Egypt Air zuwa kasar Saudia a jiya Asabar.

Dangantaka tsakanin kasashen biyu dai ya fara tsami ne a shekarar da ta gabata, kan matsalolin da suka hada da yakin da gidan sarautar Saudia take jagorantar wasu kasashen larabawa kan kasar  Yemen da kuma wasu matsalolin tsaro a yankin.

Rikicin kasashen biyu dai ya kai ga Saudia ta dakatar da sayarwa kasar Masar danyen manfetur wanda ya tilasta mata komawa ga kasar Iraqi don sayan sa.