Ivory Coast : Kablan Ducan, Ya Yi Rantsuwar Kama Aiki
-
Mista Daniel Kablan Ducan, lokacin da yake rsantsuwar kama aiki (hoto AFP)
Tsohon firaministan kasar Ivory Coast, Daniel Kablan Duncan, ya yi rantsuwar kama aiki a matsayinsa na mataimakin shugaban kasar.
A jawabin da ya gabatar yayin rantsar dashi, Mr Kablan ya ce a shirye yake ya dafawa gwamnatin Alhasan Watara domin cimma manufofinta.
Mr Kablan dan shekaru 73 a duniya wanda aka zaba karon farko a watan daya gabata a matsayin dan majalisa a yankin Grand-Bassam dake kudancin kasar, shi ne dai mutum na farko daya fara rike mukamin mataimakin shugaban kasa a wannan kasar ta Ivory Coast.
kirkiro da mukamin mataimakin shugaban kasa, wanda shi ne mukami na biyu mafi girma a kasar ta Ivory Coast, na kunshe ne a cikin sabon kundin tsarin mulkin kasar da gwamnatin Shugaba Alhasan Watara ta gabatar wanda ya samu amuncewa daga al'ummar kasar.
A ranar 9 ga watan nan ne Mr Daniel Kablan Duncan, ya gabatar da murabus din gwamnatinsa ga shugaba Watara domin share fagen nada shi a matsayin mataimakin shugaban kasa, inda kuma aka maye gurbinsa da tsohon sakatare janar a fadar shugaban kasa Amadu Gon Kulibaly wanda aka nada firaminista a yanzu.