Jirgin Sojin Najeriya Ya Kashe Mutum 52 Bisa Kuskure
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i16756-jirgin_sojin_najeriya_ya_kashe_mutum_52_bisa_kuskure
Rundinar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa wani jirgin yakin ta ya kai hari kan kuskure kan wani sansanin 'yan gudun hijira na karamar hukumar   Kala-Balge dake jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:33+00:00 )
Jan 18, 2017 02:50 UTC
  • hoto (MSF)
    hoto (MSF)

Rundinar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa wani jirgin yakin ta ya kai hari kan kuskure kan wani sansanin 'yan gudun hijira na karamar hukumar   Kala-Balge dake jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.

Koda yake kawo yanzu rundinar sojin kasar bata fitar da nata alkaluma ba, aman rahotannin sun ce akalla mutane 52 da suka hada da fararen hula da ma'aikatan agaji suka rasa rayukansu sakamakon harin.

Kungiyar bada agaji ta Red Cross ta tabbatar da mutuwar shida daga cikin ma'aikatanta, yayin da kungiyar likitoci masu bayar da agaji ta duniya, MSF ta ce tana kula da wadanda suka jikkata guda 120.

Wasu rahotanni na daban sun ce lamarin ya kuma yi sanadin mutuwar wasu jami'an tsaro da kuma raunana wasu.

A taron manema labarai da ya kira babban kwamanda na Operation Lafia Dole, Manjo Janar Lucky Irabor ya shaida cewa, an kai harin ne bayan samun labarin cewa, ‘yan kungiyar Boko Haram na haduwa a karamar hukumar ta Kala-Balge.

''ya ce an sanar dani cewa ga 'yan boko Haram na haduwa, nan take na ce an dauki mataki, saidai kash kadara ta rigai fata, ashe akwai fararen hula a wurin'' 

A nasa bangare shugaban kasar Muhammadu Buhari ya aike da sakon nuna takaici da kuma jaje, game da asarar rayukan da aka yi.