Gambia : Jammeh, Ya Ayyana Dokar Ta Baci
(last modified Wed, 18 Jan 2017 06:21:44 GMT )
Jan 18, 2017 06:21 UTC
  • Jammeh ya shafe tsawan shekaru 22 ya na Shugabancin Gambia
    Jammeh ya shafe tsawan shekaru 22 ya na Shugabancin Gambia

Shugaban Gambia mai barin gado Yahya Jammeh ya ayyana dokar ta baci ta tsawan kwanaki 90 a kasar, a daidai lokacin da ya rage 'yan sa’oi wa’adin mulkinsa ya kare.

Jammeh ya ayyana dokar ta bacin ne bisa abunda ya kira shishigi na kasashen waje a harkar zaben kasar ta Gambia, 

Matakin na zuwa ne jim kadan bayan da Najeriya ta tura jirgin ruwan yakinta don kara matsin lamba kan Mista Jammeh, ya mika mulki cikin ruwan sanyi.

A gobe Alhamis ne ya kamata a rantsar da Adama Barrow wanda hukumar zaben kasar ta bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar da aka kada kuri'arsa a ranar 1 ga watan Disamba bara.

Tunda farko dai Jammeh ya taya Adama Barow murnar lashe zaben kafin, ana cikin hakan ne a ranar 9 ga watan Disamban ya sanar da kin amuncewa da shan kayi, bayan ya zargi jami’an hukumar zaben kasar da tafka kura-kurai a zaben.

Mista Jammeh dake shugabancin kasar ta Gambia tsawan shekaru 22 ya jaddada cewa ba zai sauka daga mulki ba har sai kotu ta yanke hukunci akan karar daya shigar.