Sabon Bore Sojoji A Kasar Ivory Coast
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i16762-sabon_bore_sojoji_a_kasar_ivory_coast
Wani sabon bore Sojoji ya sake barkewa a kasar Ivory Coast, kwanaki kadan bayan cimma wata yarjejeniya da sojojin da suka yi bore a Bouake.
(last modified 2018-08-22T06:59:33+00:00 )
Jan 18, 2017 02:52 UTC
  • Akalla sojoji 2 suka mutu a sabon boren
    Akalla sojoji 2 suka mutu a sabon boren

Wani sabon bore Sojoji ya sake barkewa a kasar Ivory Coast, kwanaki kadan bayan cimma wata yarjejeniya da sojojin da suka yi bore a Bouake.

Boren da sojoji suka fara daga birnin Zambakro, ya bazu har zuwa birane shida na kasar da suka hada da Yamoussoukro, Daloa, Man, Bondoukou, Dimbokro, da kuma Bouake inda sojoji sukayi bore kwanan baya.

Sojojin dai na nuna rashin jin dadinsu ne akan yadda yarjejeniyar ba'a saka su ba a cikin wadanda yarjejeniyar karin albashin da aka cimma.

Wasu rahotanni na daban sun ce akalla sojoji biyu ne suka rasa rayukansu a boren.

Bayanai daga kasar sun ce an daina jin karan harbe-harbe da yammacin jiya, a yayin da kuma aka shiga tattaunawa da wakilan gwamnati.

A karshen makon daya gabata ne gwamatin kasar ta sanar da cimma yarjejeniya da sojojin wadanda tsaffin 'yan tawayen da aka shigar dasu ne aikin soja wadanda sukayi bore saboda neman a kara musu albashi da kuma alawus.