Jandarmomi Masu Bore Sun Rufe Babbar Tashar Ruwan Ivory Coast
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i16789-jandarmomi_masu_bore_sun_rufe_babbar_tashar_ruwan_ivory_coast
Rahotanni daga kasar Ivory Coast sun bayyana cewar Jandarmomi masu bore sun kwace babbar tashar jiragen ruwan kasar a yau din nan Laraba da kuma tilasta wa kamfanonin da suke wajen ciki kuwa har da kamfanonin da suke sarrafa Cocoa rufe kamfanonin na su, lamarin da ke nuni da cewa har ya zuwa yanzu dai ba a kawo karshen boren da jami'an tsaron suke yi ba.
(last modified 2018-08-22T06:59:33+00:00 )
Jan 18, 2017 14:02 UTC
  • Jandarmomi Masu Bore Sun Rufe Babbar Tashar Ruwan Ivory Coast

Rahotanni daga kasar Ivory Coast sun bayyana cewar Jandarmomi masu bore sun kwace babbar tashar jiragen ruwan kasar a yau din nan Laraba da kuma tilasta wa kamfanonin da suke wajen ciki kuwa har da kamfanonin da suke sarrafa Cocoa rufe kamfanonin na su, lamarin da ke nuni da cewa har ya zuwa yanzu dai ba a kawo karshen boren da jami'an tsaron suke yi ba.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar jandarmomin - wadanda 'yan sanda ne da suke karkashin ikon ma'aikatar tsaron kasar - sun kwace babbar tashar ruwan da ke birnin Abidjan babban birnin kasar a yau bayan da suka fito daga barikinsu.

Hakan kuwa yana zuwa ne a daidai lokacin da wasu sojojin ma suka ta harbe a gaban babban gidan yarin garin Bouake, gari na biyu mafi girma a kasar ta Ivory Coast don tilasta wa gwamnatin kasar musu karin albashi.

A kwanakin baya ne dai wasu tsoffin 'yan tawayen kasar da aka shigo da su cikin rundunar soji suka kaddamar da wani bore a garin na Bouake, inda daga baya dai gwamnatin Alhasan Outtaran ta tattauna da su don biya musu bukatunsu.