Shugaba Buhari Na Tarayyar Nigeria Ya Tafi Hutun Jinya Na Kwanaki 10
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i16852-shugaba_buhari_na_tarayyar_nigeria_ya_tafi_hutun_jinya_na_kwanaki_10
Shugaban tarayyar Nigeria Muhammad Bukari ya fara hutun kwanaki 10 don jinya a kasar Britania,
(last modified 2018-08-22T06:59:34+00:00 )
Jan 20, 2017 00:26 UTC
  • Shugaba Buhari Na Tarayyar Nigeria Ya Tafi Hutun Jinya Na Kwanaki 10

Shugaban tarayyar Nigeria Muhammad Bukari ya fara hutun kwanaki 10 don jinya a kasar Britania,

Majiyar fadar shugaban kasa ta nakalto mai bawa shugaban kasa shawara na musaman kan harkokin watsa labarai Mr Femi Adesina yana fadar cewa hutun kwanaki goma wanda shugaban ya dauka yana daga cikin hutunsa na shekara shekara, 

Adesina ya kara da cewa shugaban Muhammadu Buhari zai dawo a ranarb 6 ga watan Febreru mai kamawa, kamar yadda sashe 145(i) na kundin tsarin mulkin kasar wanda aka yi wa koskorima a shekara ta 1999 ya tanada.

Adesina ya kara da cewa mataimakin shugaban kasa Yemi Asinbanjo ne zai ci gaba da ayyukan shugaban kasar a tsawon lokacin da yake hutu. Kafin ficewar shuwagaban kasar daga Nigeria a jiya dai  mataimkain shugaban kasar yana halattar taron tattalin arziki a birnin Davos na kasar Swizland. Ya kuma yanzin halattar taron don dawowa gida ya karbi aikin shugaban kasar. Wannan dai shi ne karo na ukku wanda shugaban yake zuwa kasashen wajen don jinya a cikin shekara guda.