Tawagar ECOWAS Na Tattaunawar Karshe Da Jammeh
Tawagar kungiyar ECOWAS da ta kunshi shugaban Guinea Conakry Alpha Conde, da takwaransa na Mauritania Mohamed Ould Abdoul Aziz, ta isa birnin Banjul na kasar Gambia a yunkurin shawo kan Yahya Jammeh ya mika ragamar mulki a hannun Adama Barrow a wannan rana ta juma’a.
Kafin hakan dai ECOWAS din ta baiwa Jammeh har zuwa karfe 12 na rana wannan Jumma'a domin ya mika mulki ko kuma ayi amfani da karfin soji.
Wasu rahotanni daga kasar sun ce Jammeh ya nemi a kara masa awa hudu akan wa'adin da ECOWAS ta bashi da farko, aka kuma tsawaita wa'adin ta yadda za a samu damar tattaunawar karshe.
A halin da ake ciki an baiwa dakarun sojan umarni a kan su dakatar da dannawar da suke yi cikin kasar har sai an kammala tattaunawa.
A Jiya Alhamis ne aka rantsar da Adama Barrow a ofishin jakadancin Gambia dake Senegal a mastayin shugaban kasar ta Gambia, bayan da hukumar zaben kasar ta bayyana shi a mastayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar na ranar 1 ga watan Disamba na shekara data gabata.
Wasu rahotanni na daban dake fitowa daga kasar ta Gambiya sun ce sojoji Gambiya hadin gwiwa dana kungiyar ECOWAS sun kewaye kauyen Kanilaï mahaifar shugaba mai barin gado Yahya Jammeh.