Dakarun Tsaron Kenya Sun Hallaka 'Yan Ta'addar Ashabab
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i169-dakarun_tsaron_kenya_sun_hallaka_'yan_ta'addar_ashabab
A Wani Faramaki da Suka kai Dakarun tsaron kasar kenya Sun hallaka mayakan Ashaban A Arewacin kasar
(last modified 2018-08-22T06:57:45+00:00 )
Feb 02, 2016 12:08 UTC
  • Dakarun Tsaron Kenya Sun Hallaka 'Yan Ta'addar Ashabab

A Wani Faramaki da Suka kai Dakarun tsaron kasar kenya Sun hallaka mayakan Ashaban A Arewacin kasar

Kamfanin dillancin Labaran Rauteus ya nakalto Nelson Marawa jami'in Gwamnatin jihar Lamu dake arewacin kenya na cewa Dakarun tsaron kasar sun samu nasarar hallaka wasu mutane 4 da aka kyautata zaton mayakan kungiyar Ashabab ne a tsaunukan arewacin kasar, kuma wannan na daga cikin farmakin da Dakarun tsaron kasar suka gabatar na yaki da ta'addanci.

A watan Satumba na Shekarar da ta gabata ce , aka kafa rundunar hadin gwiwa tsakanin 'yan sanda da Sojoji domin yaki da kungiyar ta'addanicin ta Ashabab a tsaunukan jihar Lamu dake arewacin kasar, inda can nan sansanin kungiyar ta Ashabab a kasar ta Kenya.

Mista Nelson na ganin cewa wannan farmaki da Dakarun tsaron hadin gwiwar kasar ke kaiwa na da mahimancin gaske dangane da tsaron kasar, inda yaka da cewa Dakarun sun kwato wata Motar 'yan sanda da mayakan na Ashabab suka sace tare da wasu bindigogi hudu samfarin AK47.

A ranar Lahadin da ta gabata, mayakan Ashabab sun kai wani hari a kauyen Kisari dake cikin jihar jihar ta Lamu, inda suka hallaka fararen hula guda Uku.

Kungiyar Ashabab ta sanar da cewa matukar Gwamnatin Kenya ba ta janye Sojojinta daga kasar Somaliya za su ci gaba da kai hare-hare cikin kasar.