Mutane 5 Sun Mutu Sakamakon Harin Ta'addancin Al-Shabab A Kasar Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i16949-mutane_5_sun_mutu_sakamakon_harin_ta'addancin_al_shabab_a_kasar_somaliya
Rahotanni daga kasar Somaliya sun bayyana cewar alal akalla mutane biyar sun rasa rayukansu kana wasu na daban kuma sun sami raunuka sakamakon harin ta'addancin da 'yan kungiyar Al-Shabab suka kai kudancin kasar ta Somaliya.
(last modified 2018-08-22T11:29:34+00:00 )
Jan 24, 2017 11:18 UTC
  • Mutane 5 Sun Mutu Sakamakon Harin Ta'addancin Al-Shabab A Kasar Somaliya

Rahotanni daga kasar Somaliya sun bayyana cewar alal akalla mutane biyar sun rasa rayukansu kana wasu na daban kuma sun sami raunuka sakamakon harin ta'addancin da 'yan kungiyar Al-Shabab suka kai kudancin kasar ta Somaliya.

Kamfanin dillancin labaran Iran IRNA ya ba da rahoton cewa a harin da wasu 'yan bindiga 'yan kungiyar ta'addancin nan ta Al-Shabab suka kai da safiyar yau Talata yankin Shabli Safli da ke kudancin kasar Somaliyan, mutane biyar sun rasa rayukansu kana wasu kuma na daban sun sami raunuka.

Yayin da yake tabbatar da labarin kai harin, babban hafsan sojojin kasar Somaliyan Abdurrahman Ahmad ya bayyana cewar: 'Yan ta'addan sun kai harin ne da manyan makamai yankin da ke kudu maso yammacin birnin Mogadishu, babban birnin kasar Somaliyan.

Wasu shaidu dai sun ce akwai yiyuwar adadin wadanda suka rasa ransu ya karu saboda munin raunin da wasu da suka sami rauni suka samu.