Babbar Darektar Asusun (IMF) Na Ran Gadi A Afrika
-
Shugaba Buhari da Christine Lagarde, a Najeriya (hoto rumbun ajiya)
Babbar Darektar Asusun bada lamuni na duniya (IMF) wato Christine Lagarde, ta isa birnin Bangi na Jamhuriya Afrika ta Tsakiya a wani gajeran ran-gadi da ta soma a Nahiyar Afrika.
Mme Lagarde zata jagoranci wani taron manema labarai tare da shugaban kasar Afrika ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera a wannan Talata.
Wannan ziyyara ta Lagarde na zuwa wata guda bayan babban taron daya gudana a Kamaru kan kaucewa karya darajar kudin CFA a kasasshen Afrika ta tsakiya.
A taron daya gudana a ranar 23 ga watan Disamba bara kasashen yankin da suka hada da Kamaru, Congo, Afrika ta Tsakiya da Gabon da Equarorial Guineada kuma Chadi sunyi watsi da duk wani shiri na karya darajar CFA wace ake canza ta kan 655 na CFA kan Euro 1.
A wani taro kuma da masu taimakawa kasar Afrika ta Tsakiya suka gudanar a Bruxells kasashe amunta da masu zuba jari sun alkawarta baiwa kasar dallar Amurka Bilyan 2,2 a cikin shekaru uku masu zuwa domin taimaka mata farfadowa daga tabarbarewar tattalin arzikin data fuskanta saboda rikicin da kasar tafi fama dashi.
A gobe Laraba ne ake sa ran Babbar Darektar Asusun na (IMF) wato Christine Lagarde zata isa kasar Uganda a ci gaba da wannan ziyara.