'Yan Gudun Hijira Gambia Sun Fara Komawa Gida
(last modified Tue, 24 Jan 2017 18:22:48 GMT )
Jan 24, 2017 18:22 UTC
  • 'Yan Gudun Hijira Gambia Sun Fara Komawa Gida

Kimanin mutanen Gambia 8,000 ne da sukayi gudun hijira domin kaucewa rikicin siyasa kasar ne suka koma gida bayan da tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ya fice daga kasar.

Alkalumen da hukumar kula da kaura jama'a ta MDD (HCR) ta fitar a kwanan baya sun nuna cewa mutanen kasar Gambia sama da 76,000 ne sukayi gudun hijira a kasar Senegal a lokacin da tsohon shugaban kasar Yahya daya sha kayi a zaben kasar ya ki mika mulki ga Adama Barrow wanda yayi nasara a zaben.

Rikicin siyasa kasar Gambia da aka kwashe kusan makonni shidda anayi ya samo asali ne a lokacin da tsahon shugaban kasar Jammeh ya ce bai yarda da akyin da sha a zaben ba kuma yaki sauka daga karagar mulki bayan da shigar da kara akan cewa an tafka kurai kurai a zaben bayan da a farko har ma y ataya abokin hammayarsa Adama Barrow Murnar lashe zaben.

Daga karshe dai da yammacin ranar Asabar data gabata ne Yahya Jammeh ya sanar da cewa zai mika mulki ga zababen shugaban kasar kana zai fice daga kasar bayan shafe dogon lokaci na kai kawo na wasu shugabanin kungiyar ECOWAS akan rarashinsa daya mika mulki cikin ruwan sanyi ko kuma a dauki matakin soji a fitar dashi da karfi.

Shugaba Alpha Conde ne kasar Guinea da takwaransa na Mauritaniya Ahmed Uld Abdel Aziz suka shawo kan Yahya Jammeh.