Yin Kira Da A gudanar Da Zabe Mai Tsafta A Kasar Kenya.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i16975-yin_kira_da_a_gudanar_da_zabe_mai_tsafta_a_kasar_kenya.
Bukatar A gudanar Da Zabe Mai Tsafta A Kasar Kenya.
(last modified 2018-08-22T06:59:34+00:00 )
Jan 25, 2017 03:01 UTC
  • Yin Kira Da A gudanar Da Zabe Mai Tsafta A Kasar Kenya.

Bukatar A gudanar Da Zabe Mai Tsafta A Kasar Kenya.

Kasashe 25 da su ka yi taro a birnin Nairobi, sun fitar da bayani da a ciki su ka yi kira da a gudanar da zabe mai tsafta, da 'yanci a cikin kasar ta Kenya.

Bayanin ya kuma yi kira ga gwamnati da jam'iyyun siyasa da cibiyoin tsaro da dukkanin al'ummar kasar ta Kenya da su nesanci amfani da tashin hankali a yayin zaben.

Kungiyoyin tarayyar Afirka da na turai sun bayyana cewa yin zabe cikin ruwan sanyi, shi ne zai zama lamuni na aiki da sabon kundin tsarin mulkin da aka amince da shi a kasar a 2010..

Za a gudanar da zabukan gamegari ne dai a kasar ta Kenya a cikin watan Augusta na 2017 da ake ciki. Ana kuma jin tsoron sake afkuwar rikice-rikicen da su ka faru a 2007 da 2008 da ya ci rayukan mutanen kasar da dama.

A zaben na 2007, Mwai Kibaki ya shige gaban Raila Odinga da kuri'u, sai dai Odinga din ya zargi abokin hamayyar tasa da yin magudi. Wannan ne abinda ya jawo rikici a cikin kasar ta Kenya. Ya kuma juye daga rikicin siyasa zuwa na kabilanci da ya mamaye fadin kasar ta Kenya.

Kabilar kikuyu da Kibaki ya fito daga cikinta, ta yi yaki da kabilar kalenjin ta Odinga. Fiye da mutane 1500 ne aka kashe a tsakanin bangarorin biyu,kuma wasu da adadinsu ya haura  300,000 su ka zama yan gudun hijira.

A halin da ake ciki a yanzu, Uhura Kenyata shi ne shugaban kasa. Yana kuma kokarin jan hankalin mutanen kasar da su gudanar da zaben cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

Sai dai kawo yanzu ba a kai ga warware sabanin da ke tsakanin gwamnati da wakilan jam'iyyun siyasa ba duk da zaman tattaunawar da aka yi.

Daya daga cikin dalilan sabani a tsakanin 'yan siyasar, shi ne amfani da hannu wajen kidaya kuri'un da aka kada a yayin zabe. A wurin, yan hamayyar siyasa suna daukar cewa amfani da hannu wajen kidaya, zai iya bude kofar magudi.

Bugu da kari, suna cewa hukumar zaben kasar, tana goyon bayan jam'iyyar da ta ke mulki ta Uhuru.

A halin da ake ciki a yanzu, an kafa kawancen siyasa wanda ya kunshi jam'iyyun hamayya 15. Kawancen yana bada taken hadin kan kasa da zummar fada da cin hanci da rashawa da kuma talauci da rashin tsaro, domin ganin sun kayar da jam'iyyar da ta ke mulki.

Gudanar da zabe mai tsafta shi ne hanyar da kasar da za ta magance matsalolinta da su ka shafi, tattalin arziki da ta'addanci.