Sabon Shugaban Kasar Gambia Ya Bukaci A Binciki Yahya Jammeh
Sabon shugaban kasar Gambia Adama Barrow ya bukaci a binciki Yahya Jammeh tsohon shugaban kasar kan zarginsa da wawushe miliyoyin daloli daga baitulmalin kasar.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a jiya Talata Adama Barrow ya bai wa mataimakiyarsa ta farko Fatuma Jallo umarnin gudanar da bincike kan kudaden da yake zargin Yahya Jammeh ya kwashe daga baitul mali na kasar, domin daukar mataki na shari'a a kansa.
Kafin wannan lokacin dai Fatuma Jallo ta sheda wa jaridar Guardian ta kasar Birtaniya cewa, Yahya Jammeh ya sace miliyan 11 daga asusun gwamnati, haka nan kuma ya wawushe wasu kaddarorin mallakin gwamnatin kasar da ta ce a loda ma wani babban jirgin ruwa na kasar Chadi da ya tafi da su.