Mutane 28 Sun Mutu A Wani Harin Ta'addanci Da Aka Kai Somaliya
Rahotanni daga kasar Somaliya sun bayyana cewa alal mutane 28 sun mutu kana wasu kusan 50 kuma sun sami raunuka bayan wata mota dauke da bam da kuma wasu 'yan bindigia sun kai hari a wani otal a birnin Mogadishu babban birnin kasar Somaliya.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo Abdikadir Abdirahman, daraktan hukumar agaji na birnin Mogadishun yana cewa sun tabbatar da mutuwar mutane 28 da kuma raunana wasu 43 sakamakon wadannan hare-hare guda biyu da aka kai hotel din.
Tun da fari dai ministan tsaron kasar Somaliyan, Abdurazak Omar Mohamed mutane 15 ne suka rasa rayukan na su yayin wannan harin, inda kuma ya ce jami'an tsaron kasar sun hallaka maharan su hudu. Sai dai wani likita da aka kai mutanen da harin ya shafa ya ce yanayin da suke ciki yayi muni akwai yiyuwar a ci gaba da samun wadanda za su rasu.
Kungiyar ta'addancin nan ta Al-shabab ta dauki alhakin kai harin, cikin wata sanarwar da gidan radiyon Andalus da ke da alaka da 'yan ta'addan ya sanar.