Shugaba Adama Barrow Zai Koma Gambiya Gobe Alhamis
(last modified Wed, 25 Jan 2017 18:22:27 GMT )
Jan 25, 2017 18:22 UTC
  • Shugaba Adama Barrow Zai Koma Gambiya Gobe Alhamis

Wani na kurkusa da sabon shugaban kasar Gambiya Adama Barrow ya bayyana cewar a gobe Alhamis ne ake sa ran sabon shugaban zai koma kasar Gambiyan daga kasar Senegal inda ya ke zaune tun 'yan kwanaki kafin rantsar da shi da aka yi a matsayin sabon shugaban kasar.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar wani na hannun daman shugaba Barrow, Amie Bojang ya shaida masa cewar a gobe Alhamis da misalin karfe hudu na yamma ne ake sa ran shugaba Barrow zai isa birnin Banjul, babban birnin kasar Gambiyan bayan ya baro birnin Dakar, babban birnin kasar Senegal.

Bayan komawarsa gidan, shugaba Barrow zai fuskanci kalubale masu yawa da suka hada da batun tattalin arziki wanda daman ya ce zai fi ba shi muhimmanci sai kuma batun tabbatar da tsarin demokradiyya bayan shekaru 22 na mulkin mutum guda a kasar.

Shugaba Barrow dai ya tafi kasar Senegal din ne bayan da rikicin siyasa yayi kamari a kasar biyo bayan rashin amincewar da tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh yayi na ya sauka daga karagar mulki bayan wa'adin mulkinsa ya kare yana mai zargin an tabka magudi a zaban da aka sanar da cewa ya sha kaye. A ranar 19 ga watan Disamban nan ne dai aka rantsar da Mr. Barrow din a matsayin sabon shugaban kasar Gambiya a ofishin jakadancin kasar da ke kasar Senegal.