Kalubalen Dake Gaban Sabon Shugaban Kasar Gambia
-
Zababen shugaban Gambia, Adama Barrow
A wannan Alhamis ce ake sa ran sabon shugaban Gambia Adama Barrow zai koma birnin Banjul fadar gwamnatin kasar, bayan rikicin siyasa daya tilasta masa shan rantsuwar kama aiki ofishin jakadancin kasar na Senegal.
Mista Barrow zai koma Banjul ne kwanaki kadan bayan da tsohon shugaban kasar Yayha Jammey ya ficce daga Gambiyar zuwa Equatorial Guinea inda ya samu mafakar siyasa, sakamakon matsin lambar da ya fuskanta daga Kungiyar kasashen yankin yammacin Afirka ( ECOWAS).
Saidai bayan komawarsa gidan, shugaba Barrow zai fuskanci kalubale masu yawa da suka hada da batun tattalin arziki wanda daman ya ce zai fi ba shi muhimmanci sai kuma batun tabbatar da tsarin demokradiyya bayan shekaru 22 na mulkin kama karya na Mista Jammeh.
Baya ga hakan kuma Barrow, zai fuskanci kalu bale wajen kafa sabuwar gwamnati, duba da yadda tun tashin farko nadin da yayiwa Mme Fatoumata Jallow Tambajang a matsayin mataimakiyarsa wacce ta haura shekarun da kundin tsarin mulkin kasar ya kayyade, koda yake sabon shugaban kasar ya ce yana kan duba wannan batu.
Haka zalika wani babban kalubale dake gaban zababen shugaban kasar ta Gambia shi ne yadda zai aiwatar da garambawul a bangaren jami'an tsaron kasar.
Mista Barrow dai ya ce duk da Jammeh ya fice daga kasar yana da bukatar kasancewar rundinar sojin kungiyar ECOWAS musamen don aiwatar da bincike kan zargin cewa an shigo da sojojin haya da kuma muggan makamai da dama a lokacin rikicinn siyasa kasar.
A halin yanzu an kiyasta dakarun Afrika 4,000 ke cikin Gambia, wadanda za su kare lafiyar shugaban da tabbatar da zaman lafiya, a yayin da shi Barrow ya bukaci ci gaba da kasancewarsu cikin har na tsawan watanni shida, bukatar da rundinar sojojin ta ECOWAS ke dubawa.
A karshen makon daya gabata ne Jammeh ya bar Gambia sakamakon matsin lamba daga kungiyar kasashen Afirka ta Yamma wadda ta tura dakarun ta Senegal dan tabbatar da cewar tsohon shugaban ya sauka daga mulki bayan kayen da ya sha a zaben da aka gudanar a ranar 1 ga wtan Disamban bara.
Kungiyar ta ECOWAS dai ta sha kai kawo kafin shawo kan Yahya Jammet ya mika ragamar mulki ga Adama Barrow wanda hukumar zaben kasar ta bayana a matsayin wanda yayi nasara a zaben.
Daga karshe dai a cikin daren Ranar Asabar data agabata ne Jammeh ya sanar a gidan talabijin din kasar cewa zai mika mulki ga Adama Barrow sannan zai fice daga kasar don saboda kaucewa zubar da jini.
A yanzu dai kasar Equatorial Guinea ce ta sanar a hukumance cewa ta bai wa tsohon shugaban kasar Gambia, Yahya Jammeh mafakar siyasa bayan ficewar sa daga Banjul.
Bayanai masu karo da juna na cewar, akwai wata yarjejeniya da aka tsara da za ta hana binciken tsohon shugaban amma ministan harkokin wajen Senegal ya ce ba shi da masaniya akai.
Wasu mutane sun fara sukar yarjejeniyar da ta bayyana cewar gwamnatin Gambia ba za ta dauki wasu matakan da za su ci zarafin tsohon shugaban ba ko kwace ma shi kadarori ba.