Rundunar Sojin Kenya Ta Ce Ta Dakile Harin Kungiyar Al-shabab
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17065-rundunar_sojin_kenya_ta_ce_ta_dakile_harin_kungiyar_al_shabab
Rundunar sojin kasar Kenya ta sanar da cewa ta dakile wani harin kwantan bauna da mayakan kungiyar 'yan ta'aadda na Al-shabab suka kaddamar a a safiyar yau a kan wani barikin sojoji da ke yankin Kulbiyow a kudancin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:35+00:00 )
Jan 27, 2017 14:04 UTC
  • Rundunar Sojin Kenya Ta Ce Ta Dakile Harin Kungiyar Al-shabab

Rundunar sojin kasar Kenya ta sanar da cewa ta dakile wani harin kwantan bauna da mayakan kungiyar 'yan ta'aadda na Al-shabab suka kaddamar a a safiyar yau a kan wani barikin sojoji da ke yankin Kulbiyow a kudancin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Xin huwa daga birnin Nairobi na kasar Kenya ya bayar da rahoton cewa, wani mai magana da yawun rundunar sojin kasar Kenya Paul Njuguna ya sheda ma manema labarai cewa, dakarun na Kenya sun fatattaki mayakan na Al-shabab.

Ya kara da cewa yanzu haka daruruwan dakarun an Kenya sun bi sawun 'yan ta'adda domin cafke su ko halaka su.

A yau ne Abdulaziz Abu Mus'ab mai magana da yawun kungiyar ta Al-shabab ya ce sun kai hari kan barin sojin Kenya, kuma sun kashe sojoji 57, furucin da rundunar sojin kasar ta Kenya ta karyata.