Al'Shabab Ta Ce Ta Kashe Sama Da Sojojin Kenya 60
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17097-al'shabab_ta_ce_ta_kashe_sama_da_sojojin_kenya_60
Kungiyar Al'shaba ta ce ta kashe Sojojin Kenya sama da 60 a wani hari da mayakanta suka  kai a kan sansanin sojin wanzar da zaman lafiya na AU da ke Somaliya.
(last modified 2018-08-22T11:29:36+00:00 )
Jan 28, 2017 06:37 UTC
  • Al'Shabab Ta Ce Ta Kashe Sama Da Sojojin Kenya 60

Kungiyar Al'shaba ta ce ta kashe Sojojin Kenya sama da 60 a wani hari da mayakanta suka  kai a kan sansanin sojin wanzar da zaman lafiya na AU da ke Somaliya.

Saidai da take mayar da martani kan batun rundinar sojin kasar Kenya ta ce batun farfaganda ne kamar yadda kungiyar ta sabayi a kafofin yada labarai.

Mayakan na Al'shabab dai sun ce sun kai harin ne a safiyar Jiya juma’a a barikin sojin mai suna Kolbiyow da ke karkashin ikon dakarun kasar Kenya masu aikin wanzar da zaman lafiya a Somalia.

Daya daga cikin mayakan ne ya soma tarwatsa kansa a lokacin da ya ke kokarin kutsa kai da mota a cikin barikin..

A halin da ake ciki dai babu tabas akan sahihancin bayyanan ko wanne bangare, kasancewar yadda suka musunta labarin, saidai wani dan jarida mai zamen kansa a yakin ya ce tabas an samu mutuwar sojojin Kenya masu yawa a yankin a yayin da dayewa kuma suka arce.