Taro Kan Makomar Libya A Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17105-taro_kan_makomar_libya_a_congo
Shugabannin kasashe mambobin kwamitin koli na kungiyar tarayya Afrika a kan Libya, na wani taro a Brazzaville babban birnin kasar Congo, domin duba irin gudun mawar da Afrika zata bayar wajen warware rikicin kasar ta Libya.
(last modified 2018-08-22T06:59:36+00:00 )
Jan 28, 2017 03:08 UTC
  • Taro Kan Makomar Libya A Congo

Shugabannin kasashe mambobin kwamitin koli na kungiyar tarayya Afrika a kan Libya, na wani taro a Brazzaville babban birnin kasar Congo, domin duba irin gudun mawar da Afrika zata bayar wajen warware rikicin kasar ta Libya.

Shugaba Denis Sassou-N'Guesso ne na Congo Brazaville ya kira taron a matsayinsa na shugaban kwamitin koli na kungiyar ta AU a kan rikicin kasar Libya.

Kwamitin dai na da kasashe mambobi guda biyar da suka hada da Afirka ta Kudu, Habasha, Nijar, Mauritania da kuma Congo - Brazzaville, saidai a wannan karon ana son sanya dukkan kasashen dake makoftaka da Libya a cikin kwamitin wanda yawan mambobinsa zai iya haura daga 5 zuwa 11.

Taron wanda shi ne karo na biyu tun bayan kafa wannan kwamitin na samun halatar shugabannin kasashen Chadi, NIjar, Mauritaniya, Afrika ta Kudu da kuma firaministan Aljeriya da kuma Fayez Al-Saraj na Libya dake samun goyan bayan kasashen duniya.

A karshe dai taron zai gabatar da shawarwarin daya cimma a zauren babban taron kungiyar ta tarayya Afrika ta AU da za'a soma a ranar 30 ga watan nan a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.