Taron Shugabanin Kasashen Afirka kan rikcin Libiya a Kasar Congo
Taron shugabannin kasashen Afirka da aka fara jiya juma’a a birnin Brazzaville na kasar Congo, na tattaunawa ne kan yakin basasar Libya da kuma yuyuwar shigar kungiyar wajen magance shi.
Shidai wannan taro ya samu halartar Shugabanin kasashen Afirka da dama kuma an buda shi ne kalkashin jagorancin Shugaban Kasar Congo Brazzaville Mista Denis Sassou Ngesso dake a matsayin manba a babban kwamitin kungiyar AU kan rikicin kasar Libiya.a yayin buda wannan taro Shugaba Ngesso ya bukaci mahalarta taron da su lalubo hanyar warware rikcin kasar ta hanyar tattaunawa tsakanin 'yan kasar bisa kare hadin kan Al'ummar kasar.kafin wannan taro, an gudanar da zaman farko kan rikicin kasar Libiyan a birnin Kigali na kasar Ruwanda.a halin da ake ciki, rikicin kasar Libiya ya zamanto babbar barazana na harakar tsaro ga kasashen dake makobtaka da ita. masana na ganin cewa akwai kwararen dalilai da ya sanya kasashen Afirka su nuna damuwa kan rikicin siyasa da kuma halin rashin tsaro da kasar Libiyan ke fuskanta. kafin wannan taro dai Shugaban kasar Tunusiya Beji Caid Essebsi ya bukaci kasashen Masar da Aljeriya da su gudanar da zama domin lalubo hanyar magance rikicin kasar ta Libiya.
A halin da ake ciki, samar da Gwamnati wacce za ta samu amincewar dukkanin bangarorin siyasa da kuma kabilun kasar shine ya kasance babbar matsala ga 'yan kasar.rashin amincewa da Gwamnatin hadin kan kasar wacce ta samu karbuwa daga kasashen Duniya daga wasu 'yan siyasa da kabilun kasar ya janyo babbar koma baya dangane da kokarin magance rikicin kasar ta Libiya, inda a hakikanin gaskiya Gwamnati ba ta da wani cikekken iko a sauren buranan kasar in banda Tripoli fadar milkin kasar,a bangare guda a kwai tsohuwar Gwamnatin kasar wacce keda hedkwata a gabashin kasar kuma wannan Gwamnati na samun goyon bayan Sojojin dake kalkashin ikon Janar Khalifa Haftar.baya ga wannan rikici na Siyasa a kwai kungiyoyin 'yan tawaye dake dauke da makamai da kuma suke da alaka da kungiyoyin ta'addanci na Duniya irinsu Alka'ida da IS, su dai wadannan kungiyoyi sun kasance babbar baraza ga harakokin tsaron Libiya.
Shigar wasu manyan kasashen Duniya irinsu Amurka da wasu kasashen Turai ya kara rura rikicin kasar, domin ko wannan su na kokarin kafa Gwamnati wacce za ta kasance tana jagorantar kasar daidai da manufofinsu, misali sabuwar Gwamnatin hadin kan kasar da aka kafa ta kasance bisa goyon bayan Amurka da MDD, a yayin da tsohon Janar din Khalifa Khaftar da kuma sojojin dake mara masa baya ke samun taimako da kuma goyon bayan kasar Faransa.
Masu sharhi kan harakokin siyasar kasar na ganin cewa idan aka samu sassauci na kacal landan da manyan kasashen Duniya ke yi a harakokin siyasar Kasar da kuma fahimtar juna tsakanin kungiyoyin siyasa da kabilun kasar, a kwai kyakkyawan fatan na samun sassauci ga sababin siyasar kasar.Wasu kuma na ganin cewa wannan shekara ta 2017 za ta kasance shekarar sulhu da fahimta juna tsakanin 'yan kasar ta Libiya musaman yadda kasashen dake makwabtaka da kasar suka bada himma ta musaman wajen lalubo hanyar warware rikci da kuma sabanin dake tsakanin 'yan kasar ta hanyar Dipulpmasiya.