AU: An Gama Shirye-Shiryen Taron Shugabannin Kasashen Afirka A Ethiopia
(last modified Sun, 29 Jan 2017 05:51:58 GMT )
Jan 29, 2017 05:51 UTC
  • AU: An Gama Shirye-Shiryen Taron Shugabannin Kasashen Afirka A Ethiopia

Kungiyar Tarayyar Afirka ta sanar da cewa an gama dukkanin shirye-shiryen da ya kamata wajen gudanar da taron shugabannin kasashen Afirka karo na 28 a helkwatar kungiyar da ke birnin Addis Ababa, babban birnin kasar Ethiopia wanda za a fara a gobe.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce ana ci gaba da tarurrukan da ya kamata a gudanar a matsayin share fagen taron shugabannin Afirkan da za a gudanar da shi daga ranakun 30 zuwa 31 ga watan Janairun nan wato daga gobe da jibi.

Rahotanni sun ce tuni dai shugabannin wasu kasashen da suka hada da shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo  da na Seychelles Danny Faure, na Zambiya Edgar Lungu da na Namibiya Hage Geingob.

Har ila yau babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da shugaban Palastinawa Mahmoud Abbas su ma suna hanyar isa birnin Addis Ababan don halartar taron inda ake sa ran za su gabatar da jawabi.

Daga cikin abubuwan da shugabannin za su tattauna kai har da lamarin tsaro da kuma batun zaben sabon shugaban kungiyar Tarayyar Afirka da mataimakinsa.