Yaki Ya Sake Barkewa A Yankin Upper Nile Na Kudancin Sudan
Mummunan yaki ya sake barkewa a yankin Upper Nile na kasar Sudan ta Kudu tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawayen kungiyar Sudan People’s Liberation Movement In-Opposition (SPLM-IO) da suke da kawance da tsohon mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudun Riek Machar.
Kafar watsa labaran Africanews ta jiyo kakakin sojin kasar Sudan ta Kudun Kanar Santo Dominic ya tabbatar da barkewar yakin yana mai cewa dakarun gwamnatin suna kare kansu ne, kamar yadda kuma ya zargi 'yan tawayen da fara kai harin inda ya ce sojojin sun kashe sojojin 'yan tawayen 10 da kuma kwace makamai da yawa.
To sai dai kakakin sojojin 'yan tawayen Kanar William Gatjiath Deng ya ce sojojin gwamnatin suka fara kai musu hari, lamarin da ya tilasta musu mayar da martani.
Wasu majiyoyi dai sun ce wani adadi na sojojin dukkanin bangarori biyun sun rasa rayukansu sakamakon wannan rikici da sabon yaki da ya sake barkewa.