Sabon ta'addancin kungiyar Boko Haram
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17203-sabon_ta'addancin_kungiyar_boko_haram
Adadin Mutanan da suka rasa rayukansu sakamakon wani sabon ta'addanci na kungiyar Boko Haram a Jihar Borno dake Shiyar arewa maso gabashin Nigeria ya haura zuwa 15
(last modified 2018-08-22T06:59:37+00:00 )
Jan 31, 2017 02:18 UTC
  • Sabon ta'addancin kungiyar Boko Haram

Adadin Mutanan da suka rasa rayukansu sakamakon wani sabon ta'addanci na kungiyar Boko Haram a Jihar Borno dake Shiyar arewa maso gabashin Nigeria ya haura zuwa 15

Kamfanin dillancin Labaran kasar Faransa daga birnin Kano ya nakalto wadanda suka ganewa idanunsu yadda lamarin ya wakana na cewa adadin Mutanan da suka rasa rayukansu sakamakon harin kwantar baunar da mayakan boko Haram suka kai a jihar Borno a wannan Litinin ya haura zuwa 15. saidai Gwamnati ta ki ta ce uffan dangane da wannan hari.

Ma'aikatan Agaji sun sanar da cewa mayakan na kungiyar Boko Haram sun kai harin ne kan wasu ayarin Motoci dake samun rakiyar motocin Soja a hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, bayan da suka kashe Mutane akalla 15 tare kuma jikkata wasu da dama sun yi awan gaba da wasu Manyan Motoci guda 15.

Daya daga cikin Direbobin ya shaidawa manema Labarai cewa a yayin da suka rage tafiyar motocin saboda rashin kyan hanya, maharan sun fito daga cikin Dajin sannan suka bude masu wuta, inda nan take suka kashe Mutane 15 tare da jikkata wasu 9 na daban.

Daya daga cikin mayakan kato da gora da Gwamnatin Najeriya ta amince da su wajen yakar Boko Haram ya shaida cewa  gawawwaki akalla 24 da kuma wadanda suka jikkata da dama ne suka kai asibiti, sannan kuma wasu fasinja da dama sun yi batan Laya.