Mayakan Kungiyar Al-shabab Sun Kaddamar Da Hare-Hare A Kudancin Somalia
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17239-mayakan_kungiyar_al_shabab_sun_kaddamar_da_hare_hare_a_kudancin_somalia
Kungiyar 'yan ta'addan takfiriyyah ta Al-shabab ta kaddamar da hare-hare a kan wani sansanin sojin kasar Somalia da ke kudancin kasar, inda suka kashe akalla mutane biyu.
(last modified 2018-08-22T11:29:37+00:00 )
Feb 01, 2017 12:04 UTC
  • Mayakan Kungiyar Al-shabab Sun Kaddamar Da Hare-Hare A Kudancin Somalia

Kungiyar 'yan ta'addan takfiriyyah ta Al-shabab ta kaddamar da hare-hare a kan wani sansanin sojin kasar Somalia da ke kudancin kasar, inda suka kashe akalla mutane biyu.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai yau a birnin magadishou, mai magana da yawun rundunar sojin kasar Somalia Abdi Bareh ya sheda cewa, mayakan kungiyar ta Alshabab sun bullo da sabbin dubaru na kai hare-hare, inda suke shammatar sojojin kasar da ma na kungiyar tarayyar Afirka.

Ya ce akalla biyu daga cikin sojojin kasar Somalia sun rasa rayukansu a harin, kuma 'yan bindigar sun tsere ba tare da kame ko daya daga cikinsu ba.

Sojojin kasar ta Somalia suna aiki ne tare da dakarun kungiyar tarayyar Afirka wadanda adadinsu ya kai dubu 22.