Mutane 112 Suka Mutu A Harin Kuskure, Inji Sojin Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17285-mutane_112_suka_mutu_a_harin_kuskure_inji_sojin_najeriya
Rundinar sojin Najeriya ta ce mutane 112 ne suka rasa rayukansu a harin da wani jirginta ya kai bisa kuskure kan sansanin 'yan gudun hijira na karamar hukumar Kala-Balge dake jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:37+00:00 )
Feb 03, 2017 01:29 UTC
  • Mutane 112 Suka Mutu A Harin Kuskure, Inji Sojin Najeriya

Rundinar sojin Najeriya ta ce mutane 112 ne suka rasa rayukansu a harin da wani jirginta ya kai bisa kuskure kan sansanin 'yan gudun hijira na karamar hukumar Kala-Balge dake jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.

Harin dai na ranar 17 ga watan Janairu yayi sanadin mutuwar fararen hula da ma'aikatan agaji da dama.

A taron manema labarai da ya kira Jiya Alhamis babban kwamanda na Operation Lafia Dole, Manjo Janar Lucky Irabor ya shaida cewa, alkaluman da da suke dasu sun nuna cewa mutane 112 ne suka mutu kana wasu 97 suka raunana. 

Tunda farko dai Rundinar sojin Najeriya ta ce an kai harin ne bayan samun labarin cewa, ‘yan kungiyar Boko Haram na haduwa a karamar hukumar ta Kala-Balge.

Amman a wannan taron manema labarai Janar Irabor ya ce bisa ga yadda mayakan boko haram suka kai hari a Ran a washe garin da lamarin ya auku ya nuna cewa akwai kamshin gaskia ga bayyanan da aka samu cewa 'yan Boko haram din sun shiga yankin.

Rundinar sojin ta kuma kara neman afuwa game da al'amarin.

A kwana baya ne dai rundinar ta sanar da kafa wani kwamitin bincike daya hada bangarori da dama domin sanin hakikanin abunda ya faru.