An Gano Mutun Biyu Daukeda Cutar Zika A Angola
Hukumar lafiya ta Duniya (WHO) ta ce an gano mutun biyu dauke da cutar Zika a Angola, lamarin da ya tabbatar cewa akwai kwayoyin cutar a yankin kudancin Afrika.
Wadanda aka gano dauke da cutar sun hada da wani jinjiri da aka haifa da karamin kai da kuma mahaifiyarsa wace take dauke da kwayoyin cutar a cewar Hernando Agudelo wakilin hukumar ta WHO a Angola.
Mista Agudelo ya kara da cewa tunda aka gano cewa akwai mai nakasa ta karamin kai dake da nasaba da cutar ta Zika, hakan ya nuna cewa akwai kwayoyin cutar dake yawo a Angola a sama da watanni tara.
Matar dai na rayuwa a kauyen Bengo dake nisan kilomita 60 daga arewacin Luanda babban birnin kasar.
Dama kafin hakan hukumomin kiwan lafiya na kasar ta Angola sun sanar da gano wasu mutane biyu dauke da cutar.
Cutar wace wani nau'in sabro ke yadawa ta bulla ne a shekara data gabata inda ta yadu har zuwa kasashe 73 da suka hada dana Latine Amurka musamen Brazil da kuma Caribean.