CAN 2017 : Za'a Fafata Tsakanin Masar Da Kamaru A Wasan Karshe
A ci gaba da gasar cin kofin Afrika na 2017 da kasar Gabon ke karbar bakunci tawagar kwallon kafa ta Kamaru ta lallasa takwararta ta Ghana da ci biyu da nema a wasan da aka buga jiya na neman zuwa wasan karshe.
Dan wasa Michael Ngadeu-Ngadjui ne ya fara zura kwallo a muntina 72 na wasan bayan dawowa daga hutun lokaci.
Sai kuma dan wasa Christian Bassogog wanda ya zura kwallo na biyu a cikin muntina uku na kari akan lokaci.
Kamaru dai ta taba lashe kofin Afrika har sau hudu, inda yanzu zata buga wasan karshe ta na bakwai a tarihin gasar kwallon Afrika.
Kamaru dai zata kara da tawagar kwallon kafa ta Masar a ranar Lahadi mai zuwa a birnin Libraville na kasar Gabon.
A ranar Asabar ne dai za'a buga wasan neman mastayi na uku dana hudu tsakanin Burkina Faso da Ghana.