CAN 2017 : Wasan Neman Matsayi na Uku Tsakanin Burkina Faso Da Ghana
A ci gaba da gasar cin kofin Afrika na 2017 da kasar Gabon ke karbar bakunci yau Asabar ne tawagar kwallon kafa ta Burkina faso zata fafata da takwararta ta Ghana a neman masayi na uku dana hudu.
Tawagar kwallon kafa ta Kamaru ta fitar da Ghana daga gasar cin kofin nahiyar Afrika bayan sun tashi wasa da ci 2-0 a fafatawarsu ta Ranar Alhamis a birnin Franceville.
Kamaru dai ta taba lashe kofin Afrika har sau hudu, inda yanzu zata buga wasan karshe na bakwai a tarihin gasar kwallon kafa na Afrika.
A gobe Lahadi ne Kamaru za ta kara da Masar a matakin wasan karshe na wannan gasar ta cin kofin Afrika wadda ita ce, karo na 31.
Masar ma dai ba kanwar lasa ce ba a fagen gasar cikin kofin Afrika, koda yake ta kwashe zagaye biyu bata shiga gasar ba a shekarun baya bayan nan.
Ana dai ganin wasan zaiyi zafi kasancewar Kamaru na neman fidda haushin Masar wace ta sha doke ta a wasan karshe.