CAN 2017 : Burkina Faso Ta Samu Matsayi Na Uku
Feb 05, 2017 07:17 UTC
A ci gaba da gasar cin kofin Afrika na 2017 da kasar Gabon ke karbar bakunci, tawagar kwallon kafa ta Burkina faso ta lallasa takwararta ta Ghana da ci daya da nema a karawar neman matsayi na uku da suka buga Jiya.
Dan wasa Alain Traore ne ya baiwa kasar ta Burkina Faso wannan matsayi bayan da ya zura kwallon a mintina na 87 na wasan.
Wannan dai ya baiwa Burkina Faso samun lambar yabo ta togulla a yayin da Ghana ta samu matsayi na hudu a gasar ta cin kofin Afrika karo na 31.
Yau Lahadi ne dai za'a yi wasan karshe tsakanin Kamaru da Masar, wasan da ake ganin zai yi zafi sosai.
Tags