Zanga-Zangar Kungiyoyin Fararen Hula A Jamhuriyar Nijar.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17365-zanga_zangar_kungiyoyin_fararen_hula_a_jamhuriyar_nijar.
Zanga-Zangar Kungiyoyin Fararen Hula A Jamhuriyar Nijar.
(last modified 2019-03-18T02:12:56+00:00 )
Feb 06, 2017 02:20 UTC
  • Zanga-Zangar  Kungiyoyin Fararen Hula A Jamhuriyar Nijar.

Zanga-Zangar Kungiyoyin Fararen Hula A Jamhuriyar Nijar.

Masu zanga-zangar na kungiyoyin farar hula, a kan titunan babban birnin jamhuriyar Nijar, Yamai, sun rika bada taken nuna kin amincewa da tsadar rayuwa, da kuma girke sojojin kasashen turai a cikin kasar.

Bugu da kari, masu zanga-zangar sun zargi shugaban kasar da rashin iya tafiyar da mulki, tare da yin kira a gare shi da ya soke bai wa kamfanin Bollore na Faransa hakkin tattara kudaden fito, wanda aka kulla yarjejeniya da shi a shekarar 2014.

A ranar 21 ga watan Decemba na 2016 ma an gudanar da Zanga-zangar a cikin birnin na Yamai. Ita ma gwamnati ta gayyato magoya bayanta domin yin wata zanga-zangar ta maida martani ga ta farko wacce su ka yi a ranar 8 ga watan janairu.

Yawaitar zanga-zangar da ake yi ta nuna kin jinin gwamnati za ta iya zama mai dauke da sakamako ga gwamnati anan gaba. Domin a halin da ake ciki a yanzu da akwai matsalolin da kasar ta fuskanta a fagegen tsaro –saboda boko-haram- da tattalin arziki, da kuma siyasa.

A baya, kawancen jam'iyyun hamayya, ( Copa) sun sanya alamar tambaya akan halarcin zaben da aka gudanar wanda ya bai wa Muhammadu Yusuf damar lashe wa, saboda karancin kayan aiki a lokacin da ake kada kuri'a.

 

Rashin tsaro na daga cikin kalubalen da ya ke gaban kasar, wanda kawo ya zuwa yanzu ba a kai ga magance shi ba. Yankin Difa na daga cikin wanda ya ke fuskantar munanan hare-haren Boko haram, wanda baya ga kashe mutane da jami'an tsaro daga lokaci zuwa lokaci, sun maida wasu da dama, zama 'yan gudun hijira. A dalilin haka aka kafa dokar ta baci a cikin yankin.

Jamhuriyar Nijar tana tsakiyar kasashen da su ke fama da rashin tsaron kamar kasar Mali da arewa da Libya a kudu. A wannan yankin, ana hada-hadar  muggan kwayoyi da makamai da kuma hijira wacce ba bisa doka ba. Wannan wani kalubale ne mai girma a gaban gwmanatin kasar.

 

Wani abu da ya jawo fushin al'ummar kasar shi ne yarjeniyoyi da aka kulla a tsakanin gwamnatin kasar da kasar Faransa. Kafa sansanonin sojan Faransa da Amurka da kuma Jamus da sunan fada da ayyukan ta'addanci, suna cikin jerin abubuwan da su ka fusata al'ummar jamhuriyar ta Nijar.

 

Al'ummar kasar suna da masaniya akan manufofin 'yan mulkin mallaka akan kasar, wanda su ke son ganin shugaban kasa ya taka musu birki. Kasashen yammacin turai, suna  gasa ne da kasar Sin, wajen ganin sun sami iko akan albarkatu masu kima da kasar ta ke da su, kamar sanadarin urani'um.

 

Bugu da kari, kasashen na turai sun samar da sansanonin soja ne a cikin kasar ta Nijar, domin hana 'yan gudun hijira ba bisa doka ba, shiga kasashensu.

Ga dukkanin alamu, rashin jin dadin da mutanen kasar su ke da yi akan yadda ake tafiyar da siyasa da rashin gamsuwa ta tattalin arziki,sannan kuma da damuwa akan matsalar tsaro, za su yin baraza ga gwamnatin  shugaba Muhammadu Yusufu.